[Kannywood] Masu Shirin Hausa sunfara Samun kwarewa a Los Angeles

0

Wasu daga cikin fitattun taurarin ‘yan wasan Kannywood da wasu masu shiryawa da ba da umarni a fina-finan Hausa suna ci gaba da samun horo a Amurka.

‘Yan wasan sun ce makarantar koyar dabarun shirya fina-finai da ke cibiyar shirin fim ta LA Studio Center.

Wannan ziyara ta zo ne a lokacin da ake shirin bikin bayar da kyatuttuka na Kannywood Awards a watan Maris, da kuma bikin cika shekaru 25 da soma fina-finan Hausa a Najeriya.

A yayin ziyarar, za su ga yadda ake shirya fim na zamani, za kuma su koyi sababbin dabaru na shirin fim wanda zai taimaka wa fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.

Share.

About Author

Leave A Reply