Kannywood: Taƙaitaccen Tarihin Mawaki Mai Muryar Zinare Wato Nazifi Asnanic

0

A ci gaba da muke na kawo maku fitattun mutane a farfajiyar masana’antar fina-finan Hausa watau Kannywood yau ma muna dauke da shahararren mawakin nan Nazifi Asnanic.

Cikakken sunan sa Nazifi Abdussalam ne kuma an haife shi a garin Kano ne kimanin shekaru 35 da suka shude.

Asnanic, kamar yadda aka fi saninsa a duniyar fim, shahararren mawaki ne wanda yayi fice da zarra a tsakanin sa’annin sa musamman ma a kasar Hausa.

HAUSATOP.com ta samu labarin cewa har ma abokan aikin sa suna yi masa kirari da inkiya cewa shine mai muryar zinare saboda yadda yake rera waka mai dadi.

An dai ce ya fara wakar sa ne tun yana dan shekara 15 a duniya kuma wani kundin wakokin sa da ya sa ya shahara dai a cikin shekar 2009 zuwa 2010 ya sake shi wanda aka yi wa lakani da Dawo.

Nazifi yana da aure da mata daya mai suna Fatima yar Katsina da kuma yayan sa su uku Mahmud, Aryan da kuma yar autar su Maryam.

 

Share.

About Author

Leave A Reply