Kannywood: Taƙaitaccen Tarihin Samun ɗaukakan Sarkin Kannywood Ali Nuhu

0

Fitaccen dan wasan Kannywood Ali Nuhu ya dade yana tasiri akan matasa musamman masu bibiyan finafinan Hausa a yankunan Arewa da sauran kasashen Afirka masu jin yaren Hausa.

A shekarar 1974 ne aka haifi Ali Nuhu, kimanin shekaru 43 da suka gabata kenan a garin Maidguri ta jihar Borno, Ali Nuhu ya fara harkan fina finai ne a shekarar 1999, kimanin shekaru 25.

HAUSATOP.com ta ruwaito Ali Nuhu ya lashe lambobin yabo da dama wanda yasa ya zamo dan wasan din Hausa mafi shahara a nahiyar Afirka gaba daya.

 

Ali Nuhu yayi finafinai har a kasashen waje, musamman a nahiyar Turai, kamar sabbin fina finan daya fitar da a bana, don haka ya sanya shi kasancewa dan wasan daya fi tasiri a tsakanin masu kallon fina finai.

Ali Nuhu ya zama maigida ga shahararrun yan Fim da dama, kamar su Adam Zango, Sadik Sani, Abida Muhammed, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi da sauransu.

 

Ali Nuhu na da iyali, inda yake auren Maimuna Ja Abdulkadir, kuma suna da yaya guda 2.

 

Share.

About Author

Leave A Reply