Karanta Kuji: Shin Kannywood Tasamu Chanji Bayan Maryam Hiyana

0

Shekaru goma kenan da fitowar wani hoton bidiyo mai tsayin mintuna 8 a inda bidiyon yake nuna wasu matsaya guda biyu suna fasikanci- Daya wani saurayi mai suna Bobo, a hanu guda kuma, dayar ba kowa bace illa wata shahararriyar jaruma mai suna Maryam Hiyana.

Wannan faifan bidiyo, wanda aka dauke shi a garin Lagos ya kawo cecekuce mai yawan gasken gaske da tsegumi maras iyaka. Kuma zai iya zama wani abu da yafi kowai tasiri a industirin Kannywood domin har sai da ya janyo tsayawar harkokin finafinai na wasu shekaru.

Jim kadan bayan afkuwar hakan, ita wanda abun ya shafe ta ta tuba tayi aure, a inda wasu da yawa kuma suka bar harkar; akwai wadanda kuma aka kora domin zargin shaye-shaye da kawalci da wasu kuma wanda ake zargin fitowa da yada faifan fitowan ta hannunsu: irinsu Kubura Dakwo, Ummi Nuhu, Farida Jalal, etc.

Kamar yadda muka fada, wannan babban ishara ce amma tambayan da muke yi muku ita ce: ko Kannywood ta wa’azantu daga wannan abu? Wasu irin chanje chanje kuka lura da shi dayan dawowar harkan finafinai? Akwai wani ci gaba ta janibin tarbiyya, kaya, maganganu musamman ga jarumai mata? Meye ne yake har yanzu yake bukatar chanji?

Share.

About Author

Leave A Reply