[Labarai] Wani Dan Kunar Bakin Wake Yatayarda Bom A Kaduwar Gombi Dake Adamawa

0

Yau da safe wani dan kunar bakin wake ya tayarda bam a kasuwar buhu dake garin Gombi a arewacin jihar Adamawa.

Dan kunar bakin
waken ya yi shigar burtu zuwa cikin
kasuwar buhu dake Gombi inda ya
tayarda bam.
Tashin bam din ya yi sanadiyar
hasarar rayuka tare da jikata wasu da dama. Wanda ya tayarda bam din wai yaro ne karami wanda ya yi shigar mata.

Banda shaidu da suka gani da ido,
kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar aukuwar lamarin. Kakakin DSP Abubakar ya bukaci jama’a da su dinga kulawa koina.

Ita ma gwamnatin jihar ta bakin
kwamishanan yada labarai Ahmed Sajo ta tabbatar da harin amma bata tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukans ba kodayake wani ganao yace ya ga gawarwaki huhutare wadanda suka jikata aka kai asibiti.

Share.

About Author

Leave A Reply