NEWS: Ana Wasan Buya Tsakanin Wasu Shugabanin Arewa Da Jami’an Tsaro

0

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa har yanzu jami’an tsaro basu samu nasarar kama shuwagabannin kungiyoyin arewan nan da suka fitar da sanarwar gargadi ga yan kabilar Ibo a kwanakin baya.

Idan dai ba’a manta ba a kwanakin baya ne wasu gamayyar shuwagabannin kungiyoyin arewa suka hadu a Arewa House Kaduna inda sukayi taron manema labarai suna gargadin yan kabilar ibo dake yankin arewa da su tattara nasu inasu su fice daga arewa.

Kungiyoyin da suka sanya hannu a sanarwar sun hada da, Nastura Ashir Sharif, Arewa Citizens Action For Change; Amb. ShettimaYerima, Arewa Youth Consultative Forum; Aminu Adam, Arewa Youth Development Foundation: Alfred Solomon, Arewa Students Forum; Abdul-Azeez Suleiman, Northern Emancipation Network; Joshua Viashman, Northern Youth Vanguard, Mohammad A. Mohammad, Northern Youth Stakeholders Forum; Mohammed Tasiu Pantami, North East Assembly da kuma Nathaniel Ajegena Adigizi, North Central Peoples Front.

Sai dai kasa da kwana guda da fitar da sanarwar ne gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya umurci hukumomin tsaro su gaggauta kama matasan da suka fitar da sanarwar.

Tun bayan wannan umurni da gwamnan ya bayar duka matasan suka buya. A yayinda wasu kuma daga cikinsu suka fice daga jihar zuwa wasu jihohi.

Share.

About Author

Leave A Reply