NEWS: Gwamnan Jihar Kano Ya Canza Sunan jami’ar Kano Wato North West Zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule

18

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta zartar da hukuncin sauya sunan sabuwar jami’ar North West dake Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya bayyana gwamnatin ta dauki wannan mataki ne sakamakon gudunmuwar da marigayi Danmasanin Kano ya bayar ga jihar Kano, Arewa da Najeriya gaba daya.

An dauki wannan mataki ne biyo bayan wani zaman gaggawa da majalisar zartarwar jihar Kano ta yi a fadar gwamnatin jihar a daren Laraba 5 ga watan Yuli, kamar yadda mashwarcin gwamna Ganduje akan watsa labaru Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Haka zalika majalisar ta amince da sauya sunan titin zuwa gidan Maitama Sule daga titin Dawaki zuwa titin Yusuf Maitama Sule, yayin da shi kuma tsohon titin Yusuf Maitama Sule an canza masa suna zuwa titin Jafaru Dan Mallam.

Sanarwar ta bayyana cewar a shirye gwamna Ganduje yake ya karrama yayan jihar Kano wadanda suka bada gagarumar gudunmuwa ga jihar.

Sai dai HAUSATOP.com ta ruwaito an samu bayyananr ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin al’ummar jihar, inda hatta wasu dalibai sun soki wannan mataki, yayin wasu kuma sukayi san barka da shi.

Share.

About Author

18 Comments

  1. Hi blogger, i must say you have high quality
    posts here. Your website should go viral. You need initial traffic only.
    How to get it? Search for: Mertiso’s tips go viral

Leave A Reply