NEWS: Mahaifiyar Babban Attijiri Wato Aliko Dangote Ta Gina Wani Katafaren Masallaci

0

Mahaifiyar hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, Hajiya Mariya Sunusi Dantata ta kammala ginin wani katafaren masallacin Juma’a a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 

Majiyar HAUSATOP.com ta samu labarin ne ta cikin wata sanarwa da aka fitar, inda aka kara da bayyana Mariya na ciyar da sama da mutane gajiyayyu su 5,000 abinci a duk rana.

 

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ne ya kaddamar da Masallacin bayan ya jagoranci sallar Juma’a a cikinta, Sarkin ya jinjina ma Hajiya Mariya kan gudunmuwar da take baiwa addinin Musulunci, daga nan ya roki Allah ya saka mata da alheri.

Share.

About Author

Leave A Reply