NEWS: Shugaba Buhari Ya Aiko Da Wata Wasika Mai Ban Tausayi Zuwa Ga Yan Nijeriya (Karanta)

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga Gwamnan Kano Dr. Ganduje. Shugaban Kasar yana ta’aziyya ne ga Jama’ar Kano duka game da rashin Dan Masani. Dan Masanin Kano mutum ne mai baiwar magana har bayan ya makance Inji Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikowa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wasikar ta’aziyar tsohon Ministan Najeriya kuma Dattijon Arewa Yusuf Maitama Sule. Shugaba Buhari yace an yi babban rashi a Najeriya.

Shugaba Buhari yace Marigayin ya taimakawa Shugabannin Najeriya na farko a lokacin yana Minista. Har ya bar Duniya ba a taba samun sa da wani rashin gaskiya ba. Shugaba Buhari yace har ya bar Duniya yana koyon darasi wajen Dan Masanin Kano idan su ka zauna.

A jiya ne shi ma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya taya sauran Jama’a ta’aziyar Marigayi Ambasada Yusuf Maitama Sule da ya cika. Gwamnan yace an yi babban rashi a Najeriya.

 

Share.

About Author

Leave A Reply