RA’AYI: Anya Akwai Jarumar Fim Din Hausa Da Ta Kai Fati Moh’d Kyau, Farin Jini Da Daukaka?

0

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Fati Mohammed har yau wasu na ganin ba a yi jarumar da ta kai ta farin jini, kyau da daukaka ba a duniyar finafinan Hausa. Ban dai sani ba ko nan gaba, amma har yanzu da babu kamar ta.

Ita ce jarumar da ake dokin ganin fuskarta a fastar finafinai. Ita ce wadda har yanzu ‘yan fim suke kiran jarumai mata na yanzu da su yi koyi da ita wajen girmama nagaba da kuma sanin makamar aiki. Sannan kuma ba ta da girman kai.

Ita ce wadda murmushin ta a fim ke sa masoyan ta yin murmushi a gaske. Haka kuma ita cewa kukanta a fim ke sa masoyanta yin kuka a gaske. Ita ce wadda idan ka nuna mata kauna a fim masoyanta suke nuna maka kauna a gaske. Idan kuma ka fito a makiyinta a fim, masoyanta za su dauke ka a abokin gabarsu a gaske.

Wadannan duk yana daga cikin irin farin da daukakar da Fati Mohammed ta yi a lokacin.

Idan masu karatu za su iya tunawa, a lokacin da aka daura auren Fati da abokin sana’arta Sani Musa Mai Iska, an yi ittfakin cewa taron daurin aurenta yana daya daga cikin manyan tarukan da aka gudanar a tarihin jihar Kano. Domin ba na mancewa masoyan jarumar da dama sun zo daga jihohi daban-daban dake fadin kasar nan, har ma daga wasu kasashe mafi kusa kamar su Nijar, Chadi, Kamaru da sauransu.

Saboda irin farin jinin da Allah ya yi mata, bana mancewa a lokacin daukar fim din Hedimasta, Bashir Bala Ciroki ya fada min cewa a fim din Zarge, wanda yake birne Fati da ranta, saboda son da ake yi wa Fati a lokacin sai da ya yi bakin jini a wurin masoyanta.

Ciroki ya kara da cewa “ba na mancewa a lokacin na je kallo a Marhaba Sinima dake birnin Kano, kawai sai na ga wasu matasa rike da sanduna suka ce min su masoyan Fati Mohammed ne. Me ya sa na binne ta da ranta a fim din Zarge? Kawai sai na ga sun rufe ni da duka. Daga karshe dai da kyar na sha a hannun wadannan mutanen. Babur dina da na je da shi sai da safe aka kawo min gida”.

Ciroki ya ce ya yi mamakin irin farin jinin da Fati take da shi da har ya kai abinda aka yi cikin wasa a fim amma masoyanta sun mayar da shi kamar gaske, har ta kai ga za su daukar mata fansa.

Haka kuma kasancewar lokacin da Fati ta yi tashe waya ba ta karade gari ba, hakan ya sa duk furodusan da zai yi fim da ita, saidai ya yi asubanci ya je gidansu, inda duk furodusan da ya yi sa’a ya same ta a gida, shi zai yi aiki da ita a wannan ranar.

Wannan kadan kenan daga cikin farin jinin da Allah ya horewa Fati. Banda masoyanta wadanda idan sun ga ana azabtar da ita a fim sun dinga sharbar kuka, su a ganinsu kamar da gaske ake azabtar da ita.

Wasu masoyan nata a wancan lokacin wadanda suka hada da maza da mata, haka za su yi tattaki daga jihohin da suke domin kawowa Fati ziyara har gida.

Ko a lokacin bikin ta ma, kungiyoyi daga jihohi daban-daban sun halarci bikinta. Bana mancewa daga cikin kungiyoyin masoyanta da na gani sun hada da; kungiyar ‘yan acaba masoya Fati Moh’d; kungiyar direbobi masoyan Fati Moh’d da dai sauransu, inda suka sanya riguna masu dauke da hotunanta.

Saboda farin jinin Fati, ko a lokacin da suke tashe da abokan aikinta irin su Abida Mohammed, Maijidda Abdulkadir, Fati ta fi su yawan masoya da farin jini.

Kusan za mu iya cewa daukaka da take da shi a wannan lokacin ne har ta kai ga ta yi tallar da ta yi silar tafiyar ta kasar waje ita da maigidanta a wancan lokacin Sani Mai Iska. Wanda kusan ita ce jaruma ta farko a farfajiyar fim Hausa da sana’arta ta yi sanadiyarta zuwa kasar waje.

Saidai kash! Abinda ya ragewa Fati a yanzu shine aure. Don haka babban fatana ga kyakkywar Bafulatanar jarumar shine, Allah ya ba ta miji nagari ta yi aure, wanda kuma a koda yaushe hakan shine burin Fati.

Share.

About Author

Leave A Reply