Soyayyace Silar Fara Waka Na – Inji Mawaki Umar M Sharif A Wata Hira Ta Musamman

0

Mawaki, producer kuma sabon jarumi Umar M Shareef ya bayyana cewa soyayya ce silar fara wakan shi, shi yasa ba mamaki idan mutane suka ga yafi damuwa da soyayya a wakokin shi.

A wata tattaunawa da yayi da wani gidan radio, mawakin ya bayyana cewa ya fara waka ne a lokacin da yake jiran wata yarinya yace mata yana son ta, bata dawo ba.

Jarumin ya bayyana cewa wakar da yayi “Soyayya bazan kara Ba. ….” a film din Sai Wata Rana ita da fito shi.

Kuma ya kara da cewa mutane na bukatan nishadi a finafinai, inda mawaka suka shigo kenan.

Share.

About Author

Leave A Reply