SPORT: Jay Jay Okocha Yafi Kowa Iya Murza Leda A Afirka

0

Image result for Jay Jay Okocha

Shahararren tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Liberia, George Weah, ya bayan da cewa Austin Jay Jay Okocha, shine mutumin da yafi kowane dan wasan kwallon kafa yin yadda yaso da tamola.

George Werah, ya kara da cewa babu wani dan wasan mai murza kwallon kafa da yafi Okocha, murza leda a duk fadin nahiyar Afirka, tsohon dan wasan Chelsea, din yace Okocha, nada kwarewa da gwanita a faggen tamola.

Ya kara da cewa dan wasan Ghana, Abedi Pele, fitatcen dan wasan kwallon kafa ne kuma kwararre amma bai kama kafar Austin Jay Jay Okocha.

George Weah, na mai cewa koshi kansa bai kama kafar Austin Jay Jay Okocha, yace idan dai za a murza leda ne a kasa ne toh Okocha, ya shiga gaban maza in ji George Weah.

Koda yake a tsawon lokacin da Jay Jay Okocha, yayi yana murza leda ya samu lambobin yabo saba’in da biyar (75) amma bai yi nasarar lashe kambin zakarar kwallon Afirka ba.

Share.

About Author

Leave A Reply