Tirkashi! Wacce aka ceto daga hannun Boko Haram ta tsere ta koma wajen mijinta dan Boko haram

0

Matar wani kwamandan Boko Haram, Aisha, da aka ceto ta tsere daga gidansu da ke Maiduguri ta koma wajen mijinta dan Boko Haram da ke dajin Sambisa.

Kana ta tafi da yarin da haifa ma dan Boko Haram din mai suna Mamman Nur.

Ta arce ne bayan fitowa daga shirin gwamnatin tarayya na wayar musu da kai bayan an cetosu daga hannun Boko Haram.

Yar uwarta, Bintu Yerima, ta bayyana cewa Aisha ta kwashe kayayyakinta ne bayan ta amsa wani kira a waya.

Tace: “Kafin ta tafi, ta amsa wayan wata mata wacce ke tare da ita a shirin. Maan tace sun koma dajin Sambisa”.

Bintu tace bayan arcewanta, Aisha ta ki amsa wayanta, a karshe ma kashe wayan tayi.

Share.

About Author

Leave A Reply